-
IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Ya Yi Ajalin Mutum 18 A Masar
Sep 12, 2017 05:49Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ko kuma Da'esh ta dauki alhakin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 a yankin Sina na kasar Masar.
-
'Yan Sandan Masar 18 Sun Rasu Sakamakon Harin Da'esh A Sina
Sep 11, 2017 17:54Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar wasu 'yan sandan kasar su 18 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da wasu masu dauke da makami da aka ce 'yan kungiyar Da'esh (ISIS) ne suka kai a yankin Sinai na kasar a yau din nan Litinin.
-
Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Sun Kashe Mutane 12 A Garin Karkuk Na Kasar Iraki
Sep 08, 2017 06:37Yan ta'addan kungiyar Da'ish sun aiwatar da kisan gilla kan wasu Irakawa fararen hula 12 a yankin Alhuwaijah da shiyar kudu maso yammacin garin Karkuk na kasar Iraki.
-
Sojojin Siriya Sun Kusa Kwace Garin Deir al-Zor Daga Hannun 'Yan Ta'addan Daesh
Sep 04, 2017 10:48Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar sojojin Siriya da kawayenta na dakarun Hizbullah da sauransu sun kusan kwace garin Deir al-Zor daya daga cikin manyan tungar 'yan ta'addan Da'esh a kasar bayan gagarumar nasarar da suka samu a kan 'yan ta'addan a jiya Lahadi.
-
Ayatullah Shahrudi: Kungiyar Da'esh Makamin Yakar Musulmi Ne A Hannun Amurka.
Sep 01, 2017 19:19Shugaban majalisar fayyace maslahar musulunci ta Iran Ayatullah Mahumud Hashimi Shahrudi ya ci gaba da cewa Amurkan tana amfani da kungiyar 'yan ta'addar ta Da'esh ne domin kawar da yunkurin musulunci.
-
Sayyid Nasrallah: Za Mu Gutsure Hannun Duk Wanda Ya So Wuce Gona Da Iri Kan Labanon
Aug 31, 2017 17:56Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen masu son wuce gona da iri kan kasar Labanon da cewa za su debi kashinsu a hannu don kuwa lokacin wuce gona da irin ya wuce.
-
Firayi Ministan Iraki Ya Sanar Da Kwato Garin Tel Afar Daga Hannun 'Yan Ta'addan Da'esh
Aug 31, 2017 17:55Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da cewa dakarun kasar sun sami nasarar kwato dukkanin garin Tel Afar da kuma dukkanin lardin Ninawah na kasar daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Da'esh da ke rike da lardin na tsawon lokaci.
-
Iraki: An Kashe 'Yan Da'esh 130 Da Suke Gudu Daga Talla'afar
Aug 30, 2017 06:56Sojojin Peshmarga na Kurdawa ne suka sanar da kashe 'yan Da'esh da suka gudo daga garin Talla'afar.
-
Dakarun Kurdawar Kasar Iraki Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Fiye Da 130
Aug 29, 2017 18:56Dakarun yankin Kurdawa mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Iraki sun kashe mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish fiye da 130 a kokarin da 'yan ta'addan suke yi na tsallakawa cikin kasar Siriya bayan da aka fatattake su daga garin Tala'afar na Iraki.
-
Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai
Aug 29, 2017 05:40Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka fatattaka daga kan iyakokin Siriya da Labanon ba su da wata mafita face kawai su mika kansu ga dakarun gwagwarmaya.