Pars Today
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) ne sun kashe mutane 6 a wani hari da suka kai kudancin kasar Libiya a jiya Juma'a.
Mahukunta a Tunusiya sun bayyana cewa: Macen da ta kai harin kunan bakin wake a kasar a jiya Litinin 'yar kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce.
Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin Fuqaha da ke tsakiyar kasar Libiya, inda suka kashe mutane tare da sace matasa da 'yan sanda.
Jami'an tsaron gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun kame gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin kudancin garin Sirt na kasar.
Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta aiwatar da kisan gilla kan wasu fararen hula goma a cikin gidan kurkuku da ke karkashin ikonta a lardin Dire-Zurr da ke gabashin kasar Siriya.
Kasashen Iran, Rasha, Iraki da Siriya sun sake bayyana aniyarsu ta yin musayen bayanan sirri a tsakaninsu dagane da kungiyar ta'addancin nan ta Daesh a kokarin da suke yi na fada da ta'addanci.
Wata kotun hukunta manya laifuka a Iraki, ta yanke wa wani mukadashin jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta IS hukuncin kisa.
Rundunar yansanda a Najeriya ta bayyana cewa akwai wakilan yan kungiyar Daesh a sansanonin yan gudun hijira a yankin arewa maso gabacin kasar.
Tsahon dan majalisar dattijan na Amurka -Kelly Ward daga Arizona ya ce: Tsoffin shugabannin Amurka suna da hannu wajen kirkiro kungiyar Da'esh.
Cikin wani rahoto da ta fitar a daren jiya laraba, kungiyar kare hakin bil-adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa sama 'yan kasar dubu biyar ne kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta zartawa hukuncin kisa.