Pars Today
Dakarun sa kai na hashadu-sha'abi da jami'an 'yan sandar kasar Iraki sun kadamar da ayukan tsarkake yankunan kudu maso yammacin kasar daga tsirarun 'yan ta'addar ISIS din da suka rage
Za'a gurfanar da wani tsohon jami'in yansandan Amurka a gaban kuliya a yau jumma'a a birnin Washington na kasar Amurka tare da tuhumarsa da tallafawa mayakan kungiyar yan ta'adda ta Daesh da kudade.
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya yi gargadi kan matsalar kwararowar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish zuwa yankin arewacin Afrika bayan kashin da suka sha a kasashen Siriya da Iraki.
Hukumar abinci da noma ta dunia FAO ta bada rahoton cewa kashi 40% na albarkatun noma na kasar Iraqi sun lalace sanadiyyar yaki da ta'addanci a kasar.
Wakilin shugaban kasar Rasha na musamman kan harkokin kasar Afganistan ya bayyana cewa: Akwai tarin dalilai da hujjoji da suke nuni da cewar gwamnatin Amurka da kungiyar tsaro ta NATO suna da shirin bada mafaka ga gungun 'yan ta'addan kasa da kasa a kasar Afganistan.
Dakarun Kare juyin juya halin musulinci na Iran sun hallaka 'yan ta'adda biyar tare da kame wasu 16 na daban a yammacin kasar
Wata kotu a birnin Bagadaza na Iraki ta yankewa wata 'yar asalin kasar Jamus hukuncin kisa, saboda alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
Wata Jaridar Kasar Aljeriya ta habarta cewa akwai yiyuwar kai harin ta'addanci na kungiyar Da'esh a Kasashen Afirka
Majiyar watsa labaru mai alaka da gwamnatin hadin kan kasar Libya ta ce; An kama mutumin ne agari Sart, bisa zargin yana safarar 'yan kungiyar Da'esh zuwa kadancin kasar
Sojojin Syria sun fara kai harin ne a yankunan Huzrama da Zuraify da suke gabacin da birnin Damashka, da mayakan "JaishulIslam' suke da sansani