Pars Today
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya kirayi kasar Afirka ta Kudu da ta sauya ra'ayinta dangane da ficewar da ta yi daga kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka.
Babbar jam'iyyar adawa a Gambiya ta United Democratic Party "UDP" a takaice ta sanar da sunan dan takararta a zaben shugabancin kasar mai zuwa domin kalubalantar shugaban kasar Yahya Jammeh.
Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta zarkin shugaban kasar Gambiya Yahaya Jammeh da laifi kisan masu adawa da shi a kasar.
Rahotanni suna nuni da cewa an tashi baram-baram ba tare da an cimma matsaya ba a tattaunawar farko da aka gudanar tsakanin jami'an kasashen Gambiya da Senegal don maganace matsalar kan iyaka da ke tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya nada Alieu Momarr Njai a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasar mai zamen kan ta.
Jam'iyyar (APRC) mai mulki a kasar Gambiya ta sake tsaida shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ya shafe shekaru 21 kan madafun iko a matsayin dan takara ta a zaben shugaban kasar na watan Disamba.