Gambiya : An Nada Sabon Shugaban Hukumar Zabe
Apr 15, 2016 10:51 UTC
Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya nada Alieu Momarr Njai a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasar mai zamen kan ta.
Mr Momarr dai ya maye gurbin Mustapha Carayol dake shugabancin hukumar ta CEI tun shekara 2006.
Wani kudiri da shuagab Jammeh ya sanya ma hannu ya aike da tsohon shugaban hukumar zuwa ritaya ta nan take.
wannan dai na zuwa ne a kasa da watanni takwas kafin babban zaben kasar na watan Disamba wannan shakara da shugaba Yahya Jammeh ke takara.
a wannan watan ne kuma ake gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a wannan kasa.
Tags