Amurka Ta Haramta Wa Yahya Jammeh Da Iyalansa Shiga Kasar
(last modified Tue, 11 Dec 2018 16:24:21 GMT )
Dec 11, 2018 16:24 UTC
  • Amurka Ta Haramta Wa Yahya Jammeh Da Iyalansa Shiga Kasar

Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya wa tsohon shugaban kasar Gambiya Alhaji Yahya Jammeh da iyalansa takunkumin haramta musu shiga kasar.

A wata sanarwa da Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta fitar ta ce an dauki wannan matakin saboda lamurran da suka shafi zargin rashawa da cin hanci da kuma take hakkokin bil'adama da ake zargin an tafka a yayin mulkinsa na  tsawon shekaru 22 a kasar ta Gambiya.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa baya ga tsohon shugaba Jammeh, har ila yau kuma an sanya wa matarsa Zineb Yahya Jammeh da 'ya'yansa wannan takunkumi na haramcin shiga Amurkan.

Sanarwar ta kara da cewa tun da jimawa gwamnatin Amurkan ta kuduri aniyar taimakawa gwamnatin Adama Barrow ta kasar wajen ganin lamurra sun daidaita a kasar Gambiya da kuma gudanar da mulkin cikin kwanciyar hankali.

A shekara ta 2016 ne dai tsohon shugaba Jammeh ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar bayan shekaru 22 yana mulki. A halin yanzu dai yana gudun hijira a kasar Equatorial Guinea bayan da aka tilasta masa barin mulkin.