Pars Today
A cikin wani bayani da ofishin jakadancin Lebanon A London ya fitar a yau, gwamnatin Lebanon ta nuna takaicinta kan kan matakin da Birtaniya ta dauka na haramta Hizbullah a kasar.
Kungiyar tarayyar turai ta yi watsi da matakin da gwamnatin kasar Birtaniya ta dauka na haramta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa duk wani wuce gona da iri da za ta yi kan kasar Labanon to kuwa ba zai tafi haka kawai ba tare da martani mai kaushi daga wajen kungiyar ba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya assabar kungiyar hizbullahi ta kasar Labnon ta yi Allah wadai kan harin ta'addancin da aka kai birnin Ahwaz na kudu maso yammacin kasar Iran.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya, Faisal Miqdad yayi watsi da bukatar Amurka na ficewar dakarun Iran da na Hizbullah daga kasar Siriyan yana mai cewa wannan wani lamari ne da gwamnatin Siriya ce za ta dau mataki kansa.
Ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa shuwagabanni da wasu kamfaninin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Takunkumi.
Babban magatakardar Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ya bayyana haka ne dazu da ya gabatar da jawabi bayan fara fitowar sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
Rahotanni daga kasar Labanon na nuni da cewa kungiyoyin Hibzullah da Amal da kawayensu sun sami gagarumar nasara a zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar a jiya Lahadi.
Shugaban Majalisar dokokin kasar Labnon ya bayyana zaben a matsayin zaben jin ra'ayin al'umma kan ci gaba da gwagwarmaya, kiyaye hadin kan al'ummar kasa, da kuma tsarkake kasar daga mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, a halin yanzu a cikin ikon Allah kungiyar Hizbullah ta mallaki makamai masu linzami da za ta iya kai hari da su a kan kowace kusurwa a cikin haramtacciyar kasar Isra'ila.