Gwamnatin Lebanon Ta Mayar Da Martani Kan Haramta Hizbullah A Birtaniya
A cikin wani bayani da ofishin jakadancin Lebanon A London ya fitar a yau, gwamnatin Lebanon ta nuna takaicinta kan kan matakin da Birtaniya ta dauka na haramta Hizbullah a kasar.
Jaridar Al-akhabra ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da da ofishin jakadancin na Lebanon a London ya fitar, gwamnatin Lebanon da al'ummar kasar ba su taba amincewa da duk wani mataki irin wannan akan kungiyar Hizbullah ba.
Bayanin ya ce kungiyar tana a matsayin wani bangare mai matukar muhimamnci a kasar Lebanon, kamar yadda take da wakilci a cikin gwamnati, kuma take taka rawa a cikin dukkanin sauran lamurra da suka shafi al'ummar kasar.
A nata bangaren jam'iyyar Labour ta kasar Birtaniya ta yi kakkakusar suka kan wanann mataki da gwamnatin kasar ta dauka, tare da shan alwashin cewa za ta kalubalanci hakan idan aka kai maganar a gaban majalisar dokokin kasar.