Gwamnatocin Kasashen Iran Da Lebanon Sun Fara Tattauna Batun Tsaro A Tsakaninsu
(last modified Wed, 06 Mar 2019 06:17:16 GMT )
Mar 06, 2019 06:17 UTC
  • Gwamnatocin Kasashen Iran Da Lebanon Sun Fara Tattauna Batun Tsaro A Tsakaninsu

Jakadan kasar Iran a birnin Beyrut na kasar Lebanon ya gana da ministan tsaron kasar ta Lebanon dangane da harkokin tsaro na kasashen biyu

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Muhammad Jalal-Firuzniya jakadan JMI a Beyrut ya gana da ministan tsaron kasar Eliyas Bu Sa'ab inda ya bayyana masa cewa gwamnatin JMI a shirye take ta yi aiki tare da kasar Lebanon a fagen tsaro, don cimma manufofin tsaro na ciki da wajen kasashen biyu. 

A nashi bangaren ministan tsaron kasar ta Lebanon, Eliyas Bu Sa'ab, ya bayyana godiyarsa ga tallafin da kasar Iran take bayarwa na tabbatar da tsaro a kasar Lebanon, sannan yayi fatan kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawa don fadada wannan dangantakar.

A ranar 7 ga watan Febrerun da ya gabata ne ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zirif ya ziyarci kasar Lebanon, inda ya taya gwamnati da kuma mutanen kasar murnar kafa sabuwar gwamnati, inda Zarif da tawagarsa suka gana da jami'an sabuwar gwamnatin ta Lebanon da dama.