-
An Fara Musayen Fursunoni Tsakanin Hizbullah Da Jabhatun Nusra
Aug 02, 2017 11:05Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar an fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon din da kungiyar ta’addancin nan ta Jabhatun Nusrah, inda ‘yan ta’addan suka sako wasu dakarun kungiyar Hizbullah din su uku da suka kama a bangare guda kuma gwamnatin Labanon din ta sako ‘yan kungiyar su uku da take tsare da su.
-
Sayyid Nasrallah: Hizbullah Sun Kwato Kusan Dukkanin Yankunan Labanon Dake Hannun Jabhatun Nusra
Jul 27, 2017 05:26Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar dakarun kungiyar sun kusa kwato dukkanin yankunan kasar Labanon da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra suke rike da su tsawon shekaru, yana mai jinjinawa irin namijin kokarin da dakarun kungiyar da sojojin Labanon suka yi wajen cimma wannan nasarar.
-
Hizbullah Da Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Yankunan Kan Iyaka Daga Hannun 'Yan Ta'adda
Jul 22, 2017 05:47Dakarun kungiyar Hizbullah da sojojin Siriya sun sami nasarar kwato wasu yankuna da kauyuka alal akalla guda 9 da suke kan iyakokin kasashen Siriya da Labanon daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Jabhatun Nusra a hare-haren da suka kaddamar a jiya Juma'a.
-
S. Nasrallah: Saudiyya Ta Girmama Trump Ne Don Samun Goyon Bayan Yakar Iran
May 25, 2017 18:08Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana taron da Saudiyya ta shirya don maraba da shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin wani kokari na girmama Trump din da kada kugen yaki a kan kasar Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmaya yana mai cewa hakan babu abin da zai kara musu face tsayin daka kan tafarkin da suke kai.
-
Sayyid Nasrallah: Wajibi Ne A Hukunta Saudiyya Da Amurka Saboda Kirkiro Da'esh
Feb 16, 2017 18:04Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar wajibi ne a hukunta gwamnatocin Saudiyya da Amurka saboda kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) da kuma goyon bayanta.
-
Sayyid Nasrallah: Ba Ma Cikin Damuwa Don Kuwa Sabon Shugaban Amurka Wawa Ne
Feb 12, 2017 17:14Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya gode wa shugaban kasar Amurka Donald Trump sakamakon yadda ya bayyanar da hakikanin yanayin Amurka wa duniya, yana mai cewa ba sa cikin wata damuwa don kuwa wawa ne ke mulkin Amurkan.
-
Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Kakkausar Murya Kan Kisan Jakadan Rasha A Turkiya
Dec 20, 2016 12:43Kungiyar Hizbullah ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da kisan jakadan kasar Rasha a Turkiya Andrey Karlov, tare da bayyana hakan a matsayin aikin ta'addanci.
-
Wani Janar Na Isra'ila Ya Gargadi Netanyahu Kan Shiga Yaki Da Kungiyar Hizbullah
Dec 19, 2016 10:52Tsohon shugaban majalisar tsaron Haratacciyar kasar Isra'ila Gayura Iland, ya gargadi gwamnatin Netanyahu da kada ta yi gigin shiga wani sabon yaki da kungiyar Hizbullah.
-
Sayyid Hasan Nasrallah: Dakarun Hizbullah Sun Yi Nasarar Hana Labanon Shiga Cikin Rikici
Oct 29, 2016 16:52Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kungiyar Hizbullah din ta samu nasarar kare kasar Labanon daga fadawa cikin rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya yana mai sake jaddada muhimmancin ci gaba da kiyaye tsaro da zaman lafiyar kasar.
-
Sheikh Na'im Kasim: 'Yan Ta'addan Takfiriyyah Sun Bata Sunan Musulunci A Duniya
Oct 08, 2016 17:59Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana 'yan ta'addan wahabiyyah Takfiriyyah a matsayin masu bata fuskar addinin muslunci a idon duniya.