-
Ganawar Shugabannin Kasashen Iran Da Kazakhstan A Tehran
Apr 11, 2016 16:20Shugaban kasar Kazakhstan Nur Sultan Nazarbayev ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a birnin Tehran, domin bunkasa alaka da kasar Iran a dukkanin bangarori.
-
Ministan Tsaron Iran Ya Kirayi Gwamnatin Amurka Da Ta Daina Goyon Bayan Ayyukan Ta'addanci
Apr 10, 2016 03:54Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na cewa tana barazana ga tsaron yankin Gabas ta tsakiya tana mai cewa wajibi ne Amurka ta daina goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda sannan kuma ta fice daga yanki matukar dai tana son taimakon tsaron yankin ne.
-
Dakarun Iran Sun Yi Watsi Da Tayin John Kerry Na Tattaunawa Kan Makamai Masu Linzami Na Iran
Apr 08, 2016 16:42Mukaddashin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Birgediya Janar Massoud Jazayeri yayi watsi da bukatar sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry na tattaunawa da Iran kan shirin makamanta masu linzami yana mai kiran ma'aikatar harkokin wajen na Iran da su mayar da masa da martani mai karfin gaske.
-
Ayat. Emami Kashani: Makiya Na Neman Bangaren Raunin Al'ummar Iran Ne Don Cutar Da Su
Apr 08, 2016 15:25Ayatullah Muhammad Emami Kashani, daya daga cikin mataimakan limamin Juma'ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ja kunnen al'ummar kasar da su yi taka tsantsan dangane da ci gaba da kokarin makiyansu na ganin sun cutar da su a duk lokacin da suka sami wata dama.
-
Kwamadan IRGC Na Iran: Iran Ba Za Ta Taba Bari A Rarraba Wata Kasar Musulmi Ba
Apr 06, 2016 05:11Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin kasar Siriya a fadar da take yi da 'yan ta'adda yana mai jan kunnen cewa Iran ba za ta taba bari a raba wata kasar musulmi ba.
-
Iran Ta Sanar Da Tura Wasu Sojojinta Na Musamman Zuwa Siriya
Apr 04, 2016 17:30Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tura wasu dakarun sojojinta na kasa na musamman zuwa kasar Siriya a ci gaba da taimakon da Iran take ba wa sojojin Siriya a fadar da suke yi da kungiyoyin ta'addancin da aka shigo da su kasar daga kasashen duniya daban-daban.
-
'Yan Majalisar Iran Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Shirin Makamai Masu Linzami Na Kasar
Apr 04, 2016 16:23'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran sun sake jaddada goyon bayansu ga shirin makamai masu linzami na kariya na kasar suna masu yin watsi da ihuce-ihuce da wasu kasashe suke yi kan wannan shiri na Iran.
-
Iran Ta Ja Kunnen Kasashen Da Suke Amfani Da 'Yan Ta'adda Wajen Cimma Burinsu Na Siyasa
Apr 04, 2016 05:33Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Lebanon ya gargadi kasashe da wasu bangarori musamman na siyasa da suke amfani da 'yan ta'adda a matsayin makamin cimma wasu bukatunsu na siyasa.
-
Shugaban Kasar Iran Ya Taya Muhammad Isufu Murna Sake Samun Nasarar Dare Kan Karagar Shugabancin Niger
Apr 02, 2016 16:44Shugaban kasar Iran ya taya Muhammad Isufu murnar sake samun nasarar lashen zaben shugabancin Jamhuriyar Niger a karo na biyu.
-
Abdullahiyan: Iran Za Ta Ci Gaba Da Taimako Da Kuma Goyon Bayan Palastinawa
Apr 02, 2016 04:23Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan lamurran kasashen Larabawa da na Afirka Amir Husain Abdullahiyan ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da ba ta taimako da kuma goyon bayan da ta ke ba wa al'ummar Palastinu da ake zalunta, yana mai cewa Iran tana alfahari da hakan.