-
Hamas Ta Sha Alwashin Ci gaba Da Nuna Kin Jinin Isra'ila
Nov 06, 2018 17:34Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta ce za ta ci gaba da nuna kin jinin Haramtaciyar kasar Isra'ila har sai ta cimma gurinta.
-
Zarif: Bakar Farfangar MOSSAD A Kan Iran Ba Zai Bakanta Alakar Iran Da Kasashen Duniya Ba
Nov 01, 2018 17:06Ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar kokarin bakanta sunan Iran da kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila (MOSSAD) take a idon duniya ba zai yi nasara wajen bata alakar da Iran take da shi da kasashen duniya ba.
-
Qudus : Amurka Zata Hade Ofishin Wakilcinta Na Palasdinu Dana Israila
Oct 18, 2018 17:47Amurka ta sanar da cewa zata hade ofishin wakilcinta na Palasdinu waje guda da ofishin jakadancinta na Isra'ila dake birnin Qudus, kamar yadda ministan harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo ya sanar a yau.
-
An Gurfanar Da Matar Firayi Ministan 'Isra'ila' Saboda Zargin Zamba Cikin Aminci
Oct 07, 2018 17:05An gurfanar da matar firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Sara Netanyahu, a gaban wata kotu a birnin Qudus bisa zargin almundahana da amfani da kudaden gwamnati don biyan bukatun kanta.
-
Labanon Ta Janyo Hankulan Kasashen Duniya Kan Kokarin 'Isra'ila' Na Kawo Wa Kasar Hari
Oct 02, 2018 05:55Ministan harkokin wajen kasar Labanon Gebran Bassil ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila tana neman hanyar kawo wa kasar Labanon hari ne ta hanyar gabatar da wasu dalilai na karya yana mai cewa kasar tana da hakkin kare kanta kan duk wata barazanar da 'Isra'ilan' za ta yi mata.
-
Fara Mika Makamin Kariyar Nan Na S-300 Ga Gwamnatin Kasar Siriya
Sep 30, 2018 05:52Batun harbo jirgin saman yakin kasar Rasha a kasar Siriya da aka yi, wanda Rashan ta dora alhakin hakan gaba dayansa kan haramtacciyr kasar Isra'ila ya dau wani sabon salo da kuma isar da wani sako wanda ba a yi tsammaninsa alal akalla a wannan lokacin ba. Mahunta a kasar Rashan dai sun bayyana cewar an harbo jirgin ne sakamakon yadda sojojin 'Isra'ilan' suka fake da wannan jirgin wajen kai hari kan wasu cibiyoyi na kasar Siriya.
-
Amurka Ta Zama Saniyar Ware Kan Batun Iran A Taron Majalisar Dinkin Duniya
Sep 29, 2018 13:49Tun bayan da aka fara gudanar da babban taron zauren majalisar dinkin duniya a ranar Talata da ta gabata, daya daga cikin muhimman abubuwan da suka fi daukar hankali a taron shi ne kalaman kiyayya da Trump ya yi a kan kasar Iran, da kuma irin martanin da shugaba Rauhani na kasar Iran ya mayar masa.
-
Sojojin Mamaya Na Isra'ila Sun Kashe Palasdinawa 6
Sep 28, 2018 17:41Hukumomin kiwan lafiya a Palasdinu sun sanar da shahadar Palasdinawa shida ciki har da wani matashi dan shekara 14, sanadin harbin bindiga na sojojin mamaya na Isra'ila a zirin Gaza a yau Juma'a.
-
Sojojin Mamaya Na Isra'ila Sun Kashe Palasdinawa 6
Sep 28, 2018 16:48Hukumomin kiwan lafiya a Palasdinu sun sanar da shahadar Palasdinawa shida (6) ciki har da wani matashi dan shekara 14, sanadin harbin bindiga na sojojin mamaya na Isra'ila a zirin Gaza a yau Juma'a.
-
Afirka Ta Kudu Ta Karyata Mayar Da Jakadanta Zuwa Tel Aviv
Sep 26, 2018 19:12Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta kudu a wani bayani da ta fitar tana cewa; Jakadanta a A Tel Aviv Sisa Ngombane, ya je gudanar da wasu ayyukansa ne na kashin kansa ba aiki ya koma ba