Qudus : Amurka Zata Hade Ofishin Wakilcinta Na Palasdinu Dana Israila
Amurka ta sanar da cewa zata hade ofishin wakilcinta na Palasdinu waje guda da ofishin jakadancinta na Isra'ila dake birnin Qudus, kamar yadda ministan harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo ya sanar a yau.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce karamin ofishin jakadancin nasu za'a mayar da shi a matsayin wani ofishin kula da harkokin Palasdinawa.
Wata majiya ta daban ta bayyana cewa Amurkar zata kuma soke mukamin karamin jakadanta a yankin na Palasdinu.
Tuni mahukuntan Palasdinawa suka danganta matakin da rufe karamin ofishin jakadancinta dana wakilcin jami'an diflomatsiyanta da kuma fifita mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.
Idan hakan ta tabbata zai sanya Amurka ta kasance kasa daya tilo cikin manyan kasashen duniya da basu da wakilci a yankin Palasdinawa.