Mar 21, 2019 09:51 UTC
  • Wani Matashin Bapalastine Ya Yi Shahada A Baitu-Laham

Wani matashin bapalastine ya yi shahada yayin da wasu uku na daban suka jikkata, sanadiyar buda wuta da Sojojin sahayuna suka yi a garin Baitu-laham na yankin kogin jodan

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar kiyon lafiya ta Palastinu ta ce a daren jiya laraba wani matashin Bapalastine mai shekaru 28 a Duniya ya yi shadaha sanadiyar halbi da bindiga  da jam'ian tsaron Sahayuna suka yi masa, yayin da wasu na daban kuma suke ci gaba da jiya a asibiti.

Yayin da ake shirin cikar shera guda da fara zanga-zangar neman dawo da hakin kasa, matasan Palastinawan sun dauki alwashin ci gaba da zanga-zangar har zuwa lokacin da za a kawo karshen killacewar da aka yiwa yankin Zirin Gaza.

Ana sa ran milyoyin jama'a ne za su fito a zanga-zangar mako mai zuwa na cikar shekara guda da fara zanga-zangar neman dawo da hakkin kasa a yankin na Palastinu, kuma tuni kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa suka fara gudanar da shirye-shiryen wannan zanga-zanga.

Daga ranar 30 ga watan Maris din shekarar da ta gabata zuwa yanzu, sama da Palastinawa 270 ne suka yi shahada ta hanyar harshashen jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila.

Tags