Pars Today
Kamfanin dillancin labarin Xinhua ya ambato majiyar gwamnatin kasar tana cewa; 'Yan awaren sun sace Nimboum Arung Jung wanda jami'i na al'amurran zamantakewa a yankin arewa maso gabacin kasar.
Gwamnatin Kamarun ta sanar da kirkiro wani sabon yanki na soji don tabbatar da tsaron da ake bukata yankin Yamma da Arewa maso yamma na kasar a kokarin da gwamnatin ta ke yi na fada da 'yan awaren yankunan kasar masu magana da harshen Turanci.
Kakakin dakarun tsaron kasar Kamaru sun sanar da cewa 'yan aware sun sace wani jami'in gwamnati a yankin.
Hukumomin bayar da agaji na kasa da kasa sun yi gargadi kan ci gaba da kara tabarbarewar lamurran tsaro a yankunan masu magana da harshen turancin Ingilishi a kasar Kamaru.
Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da kisan 'yan kunar bakin wake biyu da ake zaton 'yan boko haram ne a yankin Kordo dake arewacin kasar.
Kakakin rundunar sojin Kamaru ya sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kashe sojojin gwamnatin kasar uku a yankin 'yan aware masu magana da harshen turancin na kasar.
Gwamnatin Kamaru, ta ayyana dokar ta baki a yankunan masu magana da harshen turancin Ingila, bisa fargabar hare hare na 'yan a ware.
Rahotanni daga kamaru na cewa mutane shida ne suka ras arayukansu a wani hari da ake kyautata zaton na 'yan kungiyar Boko Haram ne a yankin arewa mai nisa na kasar.
Gwamnatin kasar kamaru ta bayyana damuwarta da rikicin da ke faruwa a yankin da ake magana da harshen turanci daga yammacin kasar.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (HCR) ta nuna matukar damuwa dangane da matakin mahukuntan Najeriya na tisa keyar 'yan a waren Kamaru zuwa birnin Yaoude.