Boko Haram Ta Kashe Mutum Shida A Kamaru
(last modified Mon, 05 Feb 2018 15:30:46 GMT )
Feb 05, 2018 15:30 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Mutum Shida A Kamaru

Rahotanni daga kamaru na cewa mutane shida ne suka ras arayukansu a wani hari da ake kyautata zaton na 'yan kungiyar Boko Haram ne a yankin arewa mai nisa na kasar.

Wasu majiyoyi daga yankin da lamain ya faru, sun shaidawa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa, maharan sun kai harin ne a wajajen karfe 11 na daren jiya Lahadi a kauyen Hitawa dake karamar hukumar Turu a lardin Mokolo.

Bayanai sun ce maharan sun kuma kone gidaje sama da dari.

Yankin arewa mai nisa na Kamaru dai ya jima yana fama da matsalar tsaro dake nasaba da Boko Haram, inda gwamatin kasar ta jibge dakaru masu yawa don yaki da kungiyar, saidai duk da hakan akan samu hare haren ciki har da kunar bakin wake nan da cen a wasu lokuta.

Tun shekara 2014, lokacin da gwamnatin Kamaru ta kaddamar da yaki da Boko haram, kungiyar ta kashe fararen hula da sojoji 2,000 tare da kuma sace mutane kimanin dubu guda a yankin na arewa mai nisa dake raba iyaka da Najeriya a cewar wani rahoto da kungiyar dake sanya ido kan rikice rikice dake faruwa a duniya, ta International Crisis Group (ICG).