Pars Today
Wani dan kunar bakin wake dake kan Babur da ake kyautata zaton dan boko haram ne ya tarwatsa kansa a wani kauye dake wajen Maiduguri babban birnin jahar Bornon Najeriya tare da kashe akalla mutane uku da kuma jikkata wasu 18 na daban.
Rundunar sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram ta ce a wani farmaki na hadin gwiwa da suka kai tare da sojojin Kamaru a kan wuraren buyar 'yan Boko Haram, sun kashe 35 daga cikin mayakan kungiyar.
Rundunar sojin Mali ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kashe fararen hula 4 a yankin da ke arewacin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil'adama din ta ce a kalla mutane 35 ne sojojin Najeriya suka kashe ta hanyar kai hari da jiragen yaki
Jami'an tsaron kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun bude wuta akan masu Zanga-zanar nuna kin jinin shugaba Joseph Kabila.
Hukumar kwana-kwana a Jamhuriyar Czech ta sanar da bullar gobara a wani otel da ke birnin Prague fadar mulkin kasar da ta lashe rayukan mutane akalla biyu tare da raunata wasu fiye da arba'in na daban a cikin daren jiya.
Wasu 'yan bindiga dadi sun bindige alal akalla mutane 13 a wani hari da suka kai garin Ziguinchor da ke kudancin kasar Senegal
Kakakin Rundunar tsaron Masar ya sanar da cewa Sojoji 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyar fashewar Bam a yankin Sinai ta arewa.
Akalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 13 na daban suka jikkata sanadiyar harin kunar bakin wake a wata kasuwar kauye dake kusa da garin Maiduguri babban birnin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
Wata Majiyar kasar ta Demokradiyyar Congo ta ce soja daya ne ya rasa ransa da kuma yan kungiyar nan ta Mai-mai shida