Feb 02, 2018 06:23
Gwamnatin kasar Kenya ta yi watsi da umurnin wata babban kotu a kasar wacce ta bukaci ta kawo karshen dakatar da watsa shirye-shirye na wasu tashoshin talabijan guda uku masu zaman kansu, wadanda ta bada umurnin dakatar da watsa shirye-shiryensu bayan da suka soma watsa bukin rantsar da madugun yan adawar kasar Raila Odinga a ranar Talatan da ta gabata.