Kenya : An Aikata Muggan Laifuka A Lokutan Zabe_ HRW
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Human Rights Watch, ta fitar da wani rahoto dake cewa an ci zarafi da kuma aikata miyagun laifuka a lokutan zaben da ya gabata a kasar Kenya.
Rahoton da kungiyar ta fitar a jya ya ce, an aikata fyade ciki har da wadan jami'an tsaron kasar suka aikata a lokacin zaben da ya gabata.
Kungiyar ta ce ta gudanar da binciken ne a wuraren share- ka -zaune dake Nairobi da Bungoma da kuma Kisumu dake yammacin kasar, galibi wuraren da 'yan adawa suka fi rinjaye.
Daga cikin mata 65 da kungiyar ta yi hira dasu, rabinsu sun ce wandanda suka yi masu fyade na sanyeda kakin jami'an tsaro.
Ko baya ga hakan kungiyar ta ce dayewa daga cikin wadanda aka cin zarafinsu ba'a basu damar zuwa asibitoci ba ko wuraren shari'a, ta hanyar toshe hanyoyin dake kaiwa wuraren.