-
Jagora Ya Kirayi Jami'an Iran Daga Kada Su Mika Wuya Ga Bukatun Amurka
Oct 19, 2016 17:06Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kirayi jami'an kasar Iran da kada su mika wuya ga karin bukatun da Amurka take gabatarwa, yana mai cewa matukar suka yarda da hakan to kuwa za ta ci gaba da gabatar da wasu bukatun ne.
-
Jagora Ya Ja Kunne Dangane Da Makirce-Makircen Makiya A Kan Iran
Oct 02, 2016 11:19Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunne dangane da bakar aniyar makiya akan Iran cikin yaki na ruwan sanyi da ala'du da suka kaddamar a kan Iran yana mai cewa al'ummar Iran dai suna nan cikin shiri.
-
Sakon Jagora Imam Khamenei Ga Maniyyata Hajjin Bana (1437-2016)
Sep 05, 2016 09:27Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
-
Ayat. Khamenei: Yarjejeniyar Nukiliya Ya Tabbatar Da Cewa Amurka Ba Abar Yarda Ba Ce
Aug 01, 2016 10:33Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya ya tabbatar da cewar babu amfani wata tattaunawa da Amurka da kuma cewa ita ba abar yarda ba ce.
-
Dubi Cikin Jawabin Jagoran Juyin Juya Hali Wajen Bikin Tunawa Da Shekaru 27 Da Rasuwar Marigayi Imam Khumaini (r.a)
Jun 04, 2016 03:44A jiya Juma'a (03-05-2016) ce al'ummar Iran suka gudanar da bukukuwan tunawa da shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a duk fadin kasar don sake jaddada mubaya'arsu ga tafarkin juyin juya hali da ya bari.
-
Jagora Ya Gana Da Iyalan Shahid Mustafa Badruddeen
May 27, 2016 05:12Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana tsohon babban kwamandan dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Shahid Mustafa Badruddeen a matsayin wani jarumi kana kuma tsayayyen dan gwagwarmaya don haka yayi masa fatan samun karin matsayi da daukaka a wajen Allah Madaukakin Sarki.
-
Jagora: Rashin Mika Kai Ga Bukatun Amurka, Shi Ne Dalilin Kiyayyarta Ga Iran
May 23, 2016 17:24Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kin amincewar da mulkin mallakar Amurka da Iran ta yi shi ne babban dalilin kiyayyar da Amurkan take nuna wa Iran yana mai cewa a halin yanzu Iran ta kai matsayin da babu yadda ma'abota girman kan za su iya da ita.
-
Jagora Ya Zargi Wasu Shugabannin Kasashen Musulmi Da Ha'intarsu
May 19, 2016 05:27Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar wasu shugabannin kasashen musulmi suna ha'intar al'ummominsu ta hanyar aiwatar da siyasa da manufofin Amurka a kasashen musulmin.
-
Jagora Yayi Watsi Da Sanya Hizbullah Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Da Saudiyya Da Kawayenta Suka Yi
Apr 20, 2016 10:48Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga bayyana kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da wasu kasashen larabawa, bisa matsin lamba da cin hancin da kasar Saudiyya ta ba su, suka yi a matsayin kungiyar ta'addanci yana mai cewa kungiyar Hizbullah dai ta kasance abar alfaharin duniyar musulmi.
-
Jagora Ya Ja Kunnen Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Ta'addanci Da Wasunsu Suke Yi
Apr 12, 2016 17:35Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunnen wasu kasashen turai dangane da irin goyon bayan ayyukan ta'addanci da tsaurin ra'ayi da suke yi wanda ya ce a halin yanzu shika ta fara komawa kan mashekiya.