-
ICC Ta Bukaci A Gaggauta Cafke Mata Saif-Islam Ghaddafi
Jun 14, 2017 15:44Babbar mai shigar da kara ta kotun hukuntan mayan laifuka ta duniya, Fatu Bensuda ta bukaci da a gaggauta cafke mata dan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Ghaddafi, cewa da Seif al-Islam wanda wani gungun 'yan bindiga ya sanar da sake shi a ranar Juma'a data gabata.
-
Ethiopia da Masar Sun Bukaci MDD Da Ta Dakatar Da Sammaci Kama Al-Bashir
Jun 10, 2017 17:10Kasashen Ethiopia da Masar sun bukaci Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya dakatar da binciken da kuma shari'ar da Kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) ta ke yi wa shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir.
-
An Dage Shari'ar Cin Amanar Kasa Da Ake Wa Madugun 'Yan Adawam Zambiya
May 23, 2017 05:52Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Zambiya United Party for National Development (UPND) ta sanar da cewa an dage shari'ar cin amanar kasa da aka wa shugabanta Hakainde Hichilema zuwa gobe Laraba saboda rashin lafiyan da alkalin da ke shari'ar ya fuskanta.
-
An Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido A Gaban Kotun
May 02, 2017 11:15Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban wata kotun majistire da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawan, bisa wasu zargi guda hudu da suke masa da suka da kalaman tunzura mutane.
-
Kotu Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Rai Da Rai Da Aka Yankewa Hissene Habre
Apr 28, 2017 05:55Kotun musamman ta kungiyar Tarayyar Afirka ta tabbatar da hukuncin daurin rai-da-ran da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre bayan da aka same shi da aikata laifufukan yaki lokacin da ya ke kan karagar mulkin kasar Chadin.
-
Shugaban Zambiya Ya Ce Ba Zai Tsoma Baki Cikin Shari'ar Cin Amanar Kasa Da Ake Yi Wa Jagoran 'Yan Adawa Ba
Apr 16, 2017 10:58Shugaban Kasar Zambiya Edgar Lungu ya sanar da cewa ba zai tsoma baki cikin shari'ar zargin cin amanan kasa da ake yi wa madugun 'yan adawan kasar Hakainde Hichilema ba.
-
Wata Kotu Ta Mika Wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Kudin Da EFCC Ta Kama A Lagos
Apr 14, 2017 13:38Wata babbar kotun tarayya da ke garin Lagos ta amince da bukatar da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta gabatar mata na ta mika wa gwamnatin tarayyar Nijeriyan wasu makudan kudaden da ta kama da suka kai kimanin Naira biliyan 13 a unguwar Ikoyi da ke birnin na Lagos a ranar Larabar da ta gabata.
-
Afrika Ta Kudu Ta Ce Ba Ta Karya Doka Ba Saboda Kin Kama Shugaban Kasar Sudan
Apr 08, 2017 05:39Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce kasar ba ta karya doka ba saboda kin amincewa da ta yi da bukatar kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki (ICC) na ta kama mata shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al-Bashir da mika mata shi a lokacin da ya ziyarci kasar a shekara ta 2015.
-
ICC: Rikicin Da Ke Faruwa A Kongo Na Iya Zama Laifuffukan Yaki
Apr 02, 2017 04:54Babbar mai shigar da kara a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukanyaki, Fatou Bensouda, ta bayyana cewar rikicin baya-bayan nan da ke faruwa a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, ciki kuwa har da kisan gillan da aka yi wa wasu kwararrun Majalisar Dinkin Duniya yana iya zama daga cikin laifuffukan yaki
-
Afirka ta Kudu Ta Sanar da Janye Kudurinta Na Ficewa Daga Kotun ICC
Mar 10, 2017 05:48Kasar Afirka ta Kudu ta janye kudurinta na ficewa daga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka (ICC) bayan da babbar kotun kasar ta sanar da cewa kudurin da gwamnatin kasar ta dauka na ficewar daga kotun ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.