ICC Ta Bukaci A Gaggauta Cafke Mata Saif-Islam Ghaddafi
(last modified Wed, 14 Jun 2017 15:44:21 GMT )
Jun 14, 2017 15:44 UTC
  • ICC Ta Bukaci A Gaggauta Cafke Mata Saif-Islam Ghaddafi

Babbar mai shigar da kara ta kotun hukuntan mayan laifuka ta duniya, Fatu Bensuda ta bukaci da a gaggauta cafke mata dan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Ghaddafi, cewa da Seif al-Islam wanda wani gungun 'yan bindiga ya sanar da sake shi a ranar Juma'a data gabata.

Kotun ta ICC ko CPI, ta ce sammacin data fitar na a cafke mata da Seif al-Islam tun a shekara 2011 bisa zargin cin zarafin bil adama har yanzu yana aiki. 

A cewar ofishin mai shiga da kara na Libiya, hukumomin shari'a na Tripoli na ci gaba da neman Seif al-Islam, bayan da kotu birnin ta yanke masa hukuncin kisa a shekara 2015, saboda samunsa da laifin amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar kyammar mulkin mahaifinsa mirigayi Muammar Ghadaafi.

A lokacin dai Seif al-Islam bai halarci zamen kotun ba, kasancewar gungun yan bindiga na tsare da shi a birnin Zenten.

A yanzu dai kotun ta ICC ta ce tana ci gaba da bincike kan lamarin da kuma ci gaba da tuntuba domin sanin inda Seif al-Islam din ya ke, tare da kira ga hukumomin Libiya, da kwamitin tsaro na MDD da kuma kasashe da batun ya shafa dasu taimaka mata da bayyanai.