Pars Today
An kawo karshen babban taron zauren Majalisar Dinkn Duniya, karo na 73 da ya gudana a birnin New York na Amurka, inda shugabannin kasashe dana gwamnatoci suka gabatar da jawabi kan halin da duniya ke ciki.
Shugaba Emanuelle Macron, ya bayyana cewa tattaunawa da hadin gwiwa ta kasashen duniya ce hanyar magance sabanin da ake da shi da Iran.
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci daga sassan duniya sun fara isa birnin New York, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73.
A cikin wani rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar kan yaduwar cutar kwalara a wasu yankunan jamhuriyar Nijar a cikin 'yan watannin baya-bayan nan, an bayyana cewa mutane 55 ne suka rasa rayukansu.
A ci gaba da goyon al'ummar Palastinu, manbobin MDD sun amince da wani kudiri na yin alawadai da ta'addancin da yahudawan sahayoniya ke ci gaba da yi kan al'ummar Palastinu.
Kasar Ghana ta bayyana cewar ka kada kuri'ar rashin amincewa da matsayar Amurka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila a yayin zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ne don tabbatar da matsayar kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kuma kudururrukan Majalisar Dinkin Duniyan.
A daidai lokacin da gwamnatin Amurka take ci gaba da barazana ga kasashen duniya dangane da batun Kudus, kasashen Afirka suna daga cikin kasashen duniya da suka tsaya kyam wajen goyon bayan al'ummar Palastinu da kuma yin watsi da matsayar shugaban Amurkan kan birnin Kudus.
Ministan harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ya bayyana cewa: Al'ummar Palasdinu sun samu gagarumar nasara a kan bakar siyasar Amurka a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da gagarumin rinjaye kan kudurin da ya bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya janye matsayarsa ta sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
An rufe babban taron MDD karo na 72 da aka yi a hedkwatar Majalisar dake birnin New York a jiya Litinin, inda wakilan kasa da kasa suka bayyana ra'ayoyinsu kan yadda za a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba.