An Rufe Babban Taron MDD Karo Na 72
(last modified Tue, 26 Sep 2017 06:35:06 GMT )
Sep 26, 2017 06:35 UTC
  • An Rufe Babban Taron MDD Karo Na 72

An rufe babban taron MDD karo na 72 da aka yi a hedkwatar Majalisar dake birnin New York a jiya Litinin, inda wakilan kasa da kasa suka bayyana ra'ayoyinsu kan yadda za a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba.

Sauran batutuwan da shawarwarin da kasashen duniya suka bayar sun hada  da yadda za a tunkari barazanar nukiliya da sauyin yanayi da yaki da ta'addabci da kuma warware matsalar 'yan gudun hijira da dai sauransu.

Taron da ya gudana tsakanin ranakun 19 da 25 ga watan nan, ya samu halartar shugabanni da wakilai na kasashe da gwamnatoci 196, inda kuma suka gabatar da jawabai.

Adadin wadanda suka gabatar da jawabi a taron na wannan karon ya kasance mafi yawa cikin shekaru 11 da suka gabata.

Bugu da kari, an yi taron shawarwari na musamman kan batun sauyin yanayi da kuma taron kwamitin sulhu na MDD kan gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da dai sauransu.