Taron MDD Karo Na 73 A Birnin New York
Sep 24, 2018 11:24 UTC
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci daga sassan duniya sun fara isa birnin New York, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73.
Akwai batutuwa da dama da taron zai tattauna a kai da suka hada da batun Koriya ta Arewa, halin da ake a Siriya, yankin Sahel da kuma batun Iran, wadanda su ne zasu fi mamaye jawabin shugaba Trunp na Amurka.
A Gobe Talata ne, ake sa ran shugaban kasar Iran Hassan Rouhani zai yi nasa jawabi, in da zai tabo batun yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da kasar, musamman bayan ficewar Amurka daga cikinta.
Tags