An Kawo Karshen Babban Taron MDD Karo na 73
An kawo karshen babban taron zauren Majalisar Dinkn Duniya, karo na 73 da ya gudana a birnin New York na Amurka, inda shugabannin kasashe dana gwamnatoci suka gabatar da jawabi kan halin da duniya ke ciki.
A jiya Litinin shugabar babban taron MDD karo na 73 Maria Fernanda Espinosa Garces, ta jagoranci kammala muhawarar babban taron MDD, inda ta ce taron ya kammala cikin nasara.
A jawabinta na rufe taron, Madam Espinosa ta takaita sakamakon da aka cimma na babban taron zuwa guda 7, na farko ta ce ya mayar da hankali kan batun dunkulewar duniya wajen yin aiki tare domin sauke nauyin ayyukan MDDr da kuma kula da muhimmancin dake tattare da aikin gamayyar kasa da kasa a matsayin hanyar da za'a yi amfani da ita wajen tunkarar matsalolin dake shafar bil adama.