Tsayin Dakan Kasashen Afirka Wajen Tinkarar Barazanar Trump Kan Qudus
(last modified Mon, 25 Dec 2017 05:17:21 GMT )
Dec 25, 2017 05:17 UTC
  • Tsayin Dakan Kasashen Afirka Wajen Tinkarar Barazanar Trump Kan Qudus

A daidai lokacin da gwamnatin Amurka take ci gaba da barazana ga kasashen duniya dangane da batun Kudus, kasashen Afirka suna daga cikin kasashen duniya da suka tsaya kyam wajen goyon bayan al'ummar Palastinu da kuma yin watsi da matsayar shugaban Amurkan kan birnin Kudus.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a matsayin mayar da martani ga kalamai da barazanar jakadiyar Amurka ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, gwamnatin Botswana ta bayyana cewar: Matsayar kasar Botswana kan Kudus tana nan daram dinta, don haka ba za ta taba mika kai ga wata barazana da yin karen tsaye ga iko da 'yancin kan da kasar take da shi ba, tana mai cewa wadannan maganganu na jakadiyar Amurkan sun saba wa yanayi na diplomasiyya.

Cikin jawabin da ta yi a MDD, Jakadiyar Amurkan Nikki Haley ta yi barazanar cewa Amurka za ta janye taimakon kudade da ta ke ba wa kasashen da suka nuna rashin amincewarsu ga matsayar shugaban Amurka Trump na sanar da birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila. Kafin hakan ma dai shugaban Amurka yayi wannan barazanar a sakon da ya rubuta a shafinsa na Twitter da kuma wani jawabi da yayi kafin kada kuri'ar. Gwamnatin Amurkan dai tana fatan cewa ta hanyar wannan barazanar za ta sami damar tilasta wa kasashe masu tasowa da suke fama da matsaloli na tattalin arziki irin wasu kasashen Afirkan wannan matsaya ta su da kuma goyon bayanta a MDD.

To sai a fili yake cewa wannan barazanar ba ta yi wani tasiri a kan irin wadannan kasashen ba musamman ma dai kasashen Afirka, wadanda in ban da kasar Togo, babu wata kasar Afirka guda da ta goyi bayan wannan matsaya ta Trump, sauran kasashen Afirkan imma dai sun yi shiru da bakunansu ba su kada kuri'ar amincewa ko rashin amincewa ba, su din ma 'yan kadan ne, amma sauran kasashen Afirkan kan bakinsu ya zo guda wajen nuna rashin amincewa da wannan matsaya ta Trump.

Ko shakka babu wasu daga cikin wadannan kasashe na Afirka suna tsananin bukatar taimako na kudi da na soji na Amurka, to amma duk da hakan a wannan bangaren sun fifita su kiyaye mutumci da 'yancin kansu da kuma bayyanar da goyon bayansu ga wannan batu na Kudus maimakon tafiya tare da Amurka.

Ala kulli hal, wannan kuri'a da aka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya baya ga matsayinta na bayyanar da mahangar kasashen duniya kan makomar Kudus da kuma bayyanar da Amurka da 'Isra'ila' a matsayin saniyar ware, har ila yau kuma kuri'ar tana nuni da irin ci gaban da ake samu dangane da siyasar kasashen duniya musamman ma na Afirka a fagen kare mutumci da 'yancin kansu bugu da kari kan kosawar da kasashen duniya suka fara yi da bakar siyasar Amurka musamman ta wannan gwamnati ta Trump. Kamar yadda kuma hakan yana nuni da cewa duniya dai ba za ta taba yarda Kudus ta zama babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila ba.