Pars Today
Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana rashin zaman lafiya a wasu kasashe mambobinta, ne ke kara karfafa ayyukan ta'addanci musamman na kungiyar Da'esh a yankin.
Sama da bakin haure 'yan Afrika, 200 ne da ake tsare da su a wani gidan yari dake kudancin H.K. Isra'ila aka sallama a jiya Lahadi.
Kungiyar hadin kan majalisun kasashen larabawa ta sanar da cewa a gobe Alhamis za ta gudanar da wani taro na gaggawa a kasar Morocco don tattauna matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Firayi ministan kasar Aljeriya, Ahmed Ouyahia, ya bayyana cewar wasu kasashen larabawa sun kasashe zunzurutun kudaden da suka kai Dala Biliya 130 da nufin ruguza kasashen Siriya, Libiya da Yemen.
Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Aljeriya ya bayyana cewa: Rabuwar kai a tsakanin kasashen Larabawa da kokarin nuna isa da babakere kan junansu sun wurga su cikin kangin mulkin mallakar turawan kasashen yammacin Turai da Amurka.