Rabuwar Kan Kasashen Larabawa Ta Wurga su Cikin Kangin Mulkin Mallaka
(last modified Mon, 30 May 2016 18:17:34 GMT )
May 30, 2016 18:17 UTC
  • Rabuwar Kan Kasashen Larabawa Ta Wurga su Cikin Kangin Mulkin Mallaka

Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Aljeriya ya bayyana cewa: Rabuwar kai a tsakanin kasashen Larabawa da kokarin nuna isa da babakere kan junansu sun wurga su cikin kangin mulkin mallakar turawan kasashen yammacin Turai da Amurka.

Dan siyasa kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar Aljeriya Sa'leh Sawa'kar ya bayyana cewa; Kasashen yammacin Turai da Amurka suna amfani da matakin raba kan kasashen Larabawa ne domin ci gaba da wawushe musu dukiyoyi, don haka suke ingiza mai karfi wajen afkawa mai rauni lamarin da ke kara rusa karfin kasashen.

Sawa'kar ya kara da cewa: Baya ga barnata dukiyar al'umma da wasu 'yan tsirarun shugabannin kasashen Larabawa suke yi da nufin kare madafun iko da manufofinsu na siyasa, suna kuma ci gaba da yakar kasashen junansu a kokarin da suke yi na shimfida bakar siyasarsu ta kama karya kan raunanan kasashen junansu, inda a gefe guda kuma manyan kasashen yammacin Turai da Amurka suke ci gaba da kwasar ganimar arzikin kasashen na Larabawa.