Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Tana Son Komawar Syria Cikinta
Babban magatakardar kungiyar hadin kan kasashen larabawa Ahmad Abul Gaith ya fada a jiya alhamis cewa; Kasar Syria tana daga cikin wadanda su ka kafa kungiyar hadin kan kasashen larabawan
Abul-Gaith ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu ana tattauna batun komawar kasar Syria cikin kungiyar.
A cikin watan Nuwamba na 2011 ne dai kungiyar hadin kan kasashen larabawan ta sanar da dakatar da Syria daga cikinta. Sai dai a cikin watannin bayan nan kasashe mambobi na kungiyar sun fara musayar ra'ayi akan sake komawar Syria a cikin kungiyar
Wani jami'i na gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu Fatah Azzam wanda ya gana da Shugaban Majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barry ya ce; Syria ta fuskanci makirci ne da Amurka da kuma 'Yan Sahayoniya su ka kitsa mata, amma ta yi nasara akan 'yan ta'adda
Azzam ya bukaci ganin an samu karfafuwar alaka a tsakanin kasashen larabawa domin fuskantar makircin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila
Shekaru takwas kasar Syria ta dauka tana yaki da 'yan ta'addar da suka rika samun taimako daga kasashen turai da Amurka da kuma wasu na larabawa