-
'Yan Majalisar Iran Sun Gabatar Da Kuduri Kan Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 09, 2018 10:42'Yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran sun yi Allah wadai da sanarwar da shugaban Amurka yayi na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan kasar Iran suna masu gabatar da wani daftarin kuduri ga gwamnatin kasar kan yadda za a mayar wa Amurka da martani kan hakan.
-
Gwamnatin Iran Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tashin Farashin Kayayyaki
Dec 31, 2017 05:53Gwamnatin kasar Iran ta tabbatar wa al'ummar kasar cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen magance matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a kasar lamarin da ya haifar da wasu 'yan zanga-zanga a wasu garuruwa na kasar cikin 'yan kwanakin nan inda mutane suke nuna rashin amincewarsu da wannan yanayin.
-
Majalisar Kasar Iran Ta Kada Kuri'ar Amincewa Da Kudus A Matsayin Helkwatar Kasar Palastinu
Dec 25, 2017 17:10Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ta kada kuri'ar amincewa da kudurin da aka gabatar mata na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Palastinu a matsayin mayar da martani ga kudurin Amurka na sanar da birnin a matsayin babban birnin H.K. Isra'ila.
-
Majalisar Iran Ta Amince Da Kudurin Mayar Da Martani Ga Takunkumin Amurka
Aug 13, 2017 17:04'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran gaba dayansu sun amince da wani kuduri na mayar da martani ga sabbin takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran, bugu da kari kan kara kasafin kudin kera makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar suke kerawa don kare kasar daga duk wata barazana ta makiya.
-
Mutane 2 Sun Yi Shahada A Hare-Hare Kan Majalisar Iran Da Hubbaren Imam Khomeini
Jun 07, 2017 08:39'yan ta'adda sun kaddamar da hare-hare yau a kan majalisar dokokin kasar Iran da kuma hubbaren marigayi Imam khomeini (RA).
-
'Yan Majalisar Iran Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Shirin Makamai Masu Linzami Na Kasar
Apr 04, 2016 16:23'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran sun sake jaddada goyon bayansu ga shirin makamai masu linzami na kariya na kasar suna masu yin watsi da ihuce-ihuce da wasu kasashe suke yi kan wannan shiri na Iran.
-
'Yan Majalisar Iran Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Kungiyar Hizbullah
Mar 08, 2016 05:44Sama da 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran 200 ne suka nuna goyon bayansu ga kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma yin Allah wadai da matsayar da kungiyar larabawan Tekun Fasha na sanya kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.