Majalisar Iran Ta Amince Da Kudurin Mayar Da Martani Ga Takunkumin Amurka
(last modified Sun, 13 Aug 2017 17:04:37 GMT )
Aug 13, 2017 17:04 UTC
  • Majalisar Iran Ta Amince Da Kudurin Mayar Da Martani Ga Takunkumin Amurka

'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran gaba dayansu sun amince da wani kuduri na mayar da martani ga sabbin takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran, bugu da kari kan kara kasafin kudin kera makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar suke kerawa don kare kasar daga duk wata barazana ta makiya.

A zaman da 'yan majalisar suka gudanar a yau din nan Lahadi, dukkanin 'yan majalisar 240, sun kada kuri'ar amincewa da kudurin da suka kira shi kudurin mayar da martani ga "ta'addancin Amurka da kokarin mulkin mallakanta" a yankin Gabas ta tsakiya.

Kudurin dai zai bukaci gwamnatin kasar Iran da dakarun sojin kasar da su tsara da kuma fitar da wata siyasa da tinkarar siyasar take hakkokin bil'adama da Amurka take gudanarwa a duniya bugu da kari kan taimako da kuma goyon bayan kungiyoyi da mutanen da suka cutu daga takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran din. Kamar yadda kuma kudurin ya ware Dala miliyan 260 ga shirin kara karfafa makamai masu linzami na Iran da kuma wasu dala miliyan 260 ga dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci wadanda suka tura kwararrunsu zuwa kasashen Iraki da Siriya don  fada da kungiyoyin ta'addanci a can.

Wannan kuduri dai ya zo ne a matsayin mayar da martani da sabbin takunkumin da gwamnatin Amurkan ta sanya wa Iran saboda shirinta na makamai masu linzami.