Pars Today
Kakakin ma'ikatar tsaron kasar Iraki ya tabbatar da tuntubar hukumomin kasashen Siriya,Iran da Rasha kafin suka kaddamar da harin sama kan maboyar 'yan ta'addar ISIS a kan iyakar kasar da Siriya.
Kakakin fadar Kremlin ya ce ya zama wajibi Birtaniya ta nemi uziri kan zarkin da ta yi Rasha daga hukumomin Moscow.
Kamfanin dillancin labarun Sputnik ya ambato majiyar gwamnatin kasar Rasha na cewa korar jami'an diplomasiyya fiye da 100 da Birtaniya da kawayenta su ka yi zai fuskanci mai da martani.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Rasha ta sanar da cewa: Wani dan ina ga kisa ya gudanar da harbe-harbe a kan wani gida a yankin kudu maso gabashin kasar, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda.
Jami'an tsaron kasar Rasha, wacce ta yi wannan sanarwa ta kuma kame mutane hudu da su ke da alaka da kungiyar ta'addancin ta Da'esh.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya jaddada cewa: Rashin damawa da kasar Iran a fagen yaki da ta'addanci lamari ne da bai dace ba.