Kremlin:Dole Ne Kasar Birtaniya Ta Nemi Uzuri Daga Kasar Rasha
Kakakin fadar Kremlin ya ce ya zama wajibi Birtaniya ta nemi uziri kan zarkin da ta yi Rasha daga hukumomin Moscow.
Kamfanin dillancin labaran Tass ya nakalto Dimitry Peschof mai magana da yawun fadar shugaban kasar Rasha yayin yake amsa tambayoyi manema labarai a wannan Laraba ya ce Rasha za ta tilasta kasar Birtaniya ta nemi uzurinta akan zarginta da yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan mai suna Sergueï Skripal da batun ya tada kura sosai da kuma janyo takaddamar diflomatsiya tsakanin Rasha da kasashen Turai.
Mista Peschof ya tabbatar da cewa har abada gwamnatin kasar Birtaniya ba za ta iya tabbatar da zarkin da ta ke yi a kan kasarsa ba yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan.
Har ila yau kakakin fadar shugaban kasar Rasha ya ce tambayar da suke a halin da ake ciki, kan wani dalili Hukumomin Birtaniya suka dogara da shi na zarkin kasar Rasha da yunkurin kashe tsohon jami'in leken asirin na Rasha.
Takadama tsakanin biranan Landan da Moscow ta kunno kai ne tun bayan da hukumomin Birtaniyan suka zargi Rasha da cewa ta kai wa tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Viktorovich Skripal hari da makami mai guba.