Satar Bayanan Sirri Na Fasahar Sararin Samaniya Daga Kasar Rasha
Jami'an tsaron kasar Rasha sun fara gudanar da bincike akan yiyuwar satar bayanan sirri masu alaka da fasahar ilimin sararin samaniya daga kasar zuwa kasashen turai
Tashar talabijin din Sky News ta ce; jami'an tsaron sun gudanar da bincike a cibiyar "Roscosmos" mai gudanar da bincike akan fasahar sararin samaniya.
Rahoton ya ci gaba da cewa; A lokacin da shugaban kasar vladimir putin ya gana da shugaban hukumar sararin samaniya ta Rasha, da akwai dan leken asirin yammacin turai a wurin wanda ya nadi bayanai
Mahukunta a kasar ta Rasha na bayyana abin da ya faru a matsayin babbar cin amanar kasa, wacce ta shafi daukar bayanan sirri akan makamai masu linzami na kasar da suke da sauri fiye da sauti tare da mika su ga jami'an leken asirin wasu kasashe bisa kudaden masu yawa.
Hukumar sararin samaniyar kasar Rasha ta kira yi dukkanin cibiyoyinta da su bai wa masu binicke cikakken hadin kai domin su gudanar da aikinsu.