Manyan Hafsoshin Sojin Amurka Da Rasha Sun Gana Kan Batun Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i35450-manyan_hafsoshin_sojin_amurka_da_rasha_sun_gana_kan_batun_siriya
Manyan hafsohin sojin kasashen Rasha da Amurka sun gana, domin tattauna batun tsaro da kuma hadin guiwa tsakanin dakarunsu a Siriya.
(last modified 2019-03-05T04:47:45+00:00 )
Mar 05, 2019 04:47 UTC
  • Manyan Hafsoshin Sojin Amurka Da Rasha Sun Gana Kan Batun Siriya

Manyan hafsohin sojin kasashen Rasha da Amurka sun gana, domin tattauna batun tsaro da kuma hadin guiwa tsakanin dakarunsu a Siriya.

Ganawar wacce ba'a saba yin irinta ba, anyi ta ne tsakanin babban hafsan sojin na Amurka Joe Dunford da kuma takwaransa na Rasha, Valeri Guerassimov a birnin Vienna na kasar Austria a jiya Litini.

Bangarorin sun maida hankali ne kan yadda dakarun kasashensu zasuyi aiki a daidai lokacin da Amurka ta yunkuri anniyar rage yawan sojojinta a kasar ta Siriya, kamar yadda kakakin rundinar sojin Amurka Patrick Ryder ya sanar a cikin wata sanarwa.

A nata bangare kuwa ma'aikatar tsaron Rasha ta ce manyan hafsohin sojin kasashen biyu sun bayyana mahimmancin yin aiki aiki tare domin kaucewa samun sabani a fagen daga musamman kan yakin da suke da kungiyar Da'esh a Siriya.

Kasashen biyu sun kuma tattauna kan batn yarjejeniyar nan ta takaita kera makamai nukiliya dake tsakanin wacce sukayi watsi da ita a kwanan baya, duba da yadda kowannensu ke zargin juna da saba mata.