-
Najeriya: An dakile yunkurin kai harin ta'addanci A Birnin Ikko Da Ke Yammacin Kasar.
Dec 29, 2016 14:17"Yan sandan Najeriya Sun dakile wani yunkurin kai hari da bama-bamai a birnin Lagos.
-
Yan Gudun Hijira 3000 Ne Suka Koma Gidajensa Bayan Fatattakan Boko Haram A Jihar Borno
Dec 28, 2016 13:24Majiyar sojojin Nigeria ta bayyana cewa yan gudun hijira kimani 3000 suka koma gidajen bayan a arewa maso gabacin jihar Borno bayan fatattakon mayakan boko haram daga yankin
-
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Boge Dubu 50 A Kasar
Dec 28, 2016 07:51Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ta gano ma’aikatan boge akalla dubu 50 a fadin kasar wanda hakan ya ba wa gwamnatin tarayyar damar tsimin kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 200 tsawon wannan shekara ta 2016 da ke karewa.
-
Najeriya : An Gano Ma'aikatan Bogi 50,000
Dec 28, 2016 02:20Gwamnatin Najeriya ta sanar da Gano wasu ma'aikatan bogi su 50,000 lamarin daya taimaka mata wajen ceto makudan kudade da yawansu ya kai Miliyan 630 na (Euro) kwatamcin Bilyan 13 na Niara, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.
-
Sojin Nijeriya: Za'a Mai Da Dajin Sambisa Wajen Horon Sojoji
Dec 27, 2016 07:47Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya sanar da cewa za a mayar da Dajin Sambisa da ke jihar Borno a matsayin sansanin bayar da horo ga sojojin kasar bayan da sojojin suka sami nasarar kwace dajin daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a kwanakin baya.
-
Sojojin Nijeriya Sun Bude Wasu Hanyoyin Da Aka Rufe Saboda Rikicin Boko Haram
Dec 26, 2016 07:38Kwanaki biyu bayan da sojojin Nijeriya suka sami nasarar kwace babbar tungar 'yan Boko Haram a Dajin Sambisa na jihar Borno, sojojin Nijeriyan sun sake bude wasu manyan hanyoyi biyu da suka hada birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Bornon da kasashen Chadi da Nijar.
-
Rundunar 'Yan Sanda A Najeriya Ta Dauki Kwararan Matakan Tsaro Domin Bukukuwan Kirsimati
Dec 25, 2016 02:23Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta sanar da daukar kwararan matakan tsaro a dukkanin fadin kasar domin ganin an gudanar da bukukuwan kirsimati lami lafiya a kasar.
-
Sojojin Nijeriya Sun Kwace Tungar Boko Haram Na Karshe A Dajin Sambisa
Dec 24, 2016 13:15Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewa sojojin kasar sun sami nasarar fatattakar 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram daga babbar maboyarsu a dajin Sambisa wadda ke a matsayin wata alama ta kawo karshen 'yan ta'addan.
-
Shugaban Buhari Ya Bukaci Jihohi Su Biya Albashin Ma'aikata Daga Kudaden Bashi Da Aka Mayar Masu
Dec 23, 2016 05:00Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bada umurnin ga jihohin kasar su biyar albashin ma'aikata daga kudaden basussuka da aka mayar masu
-
Za'a Saki Tsohon Gwamnan Jihar Delta Daga Kurkuku A Kasar Britania
Dec 22, 2016 07:47James Ibori tsohon gwamna jihar Delta a yankin niger deltar na nigeria ya sami 'yencinsa bayan dauri na akalla shekaru 7 a wani gidan yari a kasar Britania saboda zamba da al-mundahana.