-
Mutanen Kanada Sun Bukaci Haramta Kayayyakin 'Isra'ila' A Kasar
Mar 04, 2017 05:52Rahotanni daga kasar Kanada sun bayyana cewar wani adadi mai yawan gaske na al'ummar kasar sun bukaci a haramta kayayyakin haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar a wani mataki na nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu.
-
Al'ummar Canada Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Duk Wani Matakin Haramta Kayayyakin H.K.Isra'ila
Mar 03, 2017 17:50Al'ummar kasar Canada sun bayyana goyon bayansu ga duk wani matakin haramta sayan kayayyakin da haramtacciyar kasar Isra'ila ke samarwa a matsayin jaddada goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta.
-
Isra'ila Ta Hana Wani Mai Kare Hakkin Bil Adama Shiga Palastinu
Mar 03, 2017 06:43Haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana wani babban jami'i mai sanya ido kan hakkokin bil adama na kasa da kasa shiga Palastinu.
-
'Yan Majalisa Faransa Na Son A Amunce Da Kasar Palestine
Feb 27, 2017 04:55A Faransa, 'yan majalisa 154 ne sun bukaci shugaban kasar François Hollande, akan ya amunce da samar da kasar Palestine.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Zame 'Yar Kallo Dangane Da Zaluncin Haramtacciyar Kasar Isra'ila
Feb 27, 2017 04:07A rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yana dauke da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta rusa gidajen Palasdinawa masu yawa a yankunan Palasdinawa da suke gabar yammacin kogin Jordan a makon da ya gabata lamarin da ya kara janyo rashin matsuguni ga Palasdinawa masu tarin yawa.
-
Ruhani: Matsalar Palastinu Wata Alama Ce Ta Gazawar Kungiyoyin Kasa Da Kasa
Feb 22, 2017 17:59Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar matsalar Palastinu ba matsala ce ta wata al'umma guda ba, face wata alama ce ta zalunci da take hakkoki wasu al'ummomi kana wani lamari da ke nuni da gazawar cibiyoyin kasa da kasa.
-
Mahalarta Taron Goyon Bayan Intifada Sun Bukaci Kasashen Musulmi Su Rufe Ofisoshin Jakadancinsu A Amurka
Feb 22, 2017 17:58Mahalarta taron kasa da kasa kan goyon bayan Intifadar al'ummar Palastinu da aka gudanar a nan birnin Tehran sun bukaci gwamnatocin kasashen musulmi da su rufe ofisoshin jakadancinsu da ke Amurka matukar dai gwamnatin kasar ta mayar da ofishi jakadancinta dake haramtacciyar kasar Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Qudus.
-
Majalisar.D.Duniya Da Kungiyar Arab League Sun Jaddada Goyon Bayansu Kan Kafa Kasar Palasdinu
Feb 17, 2017 04:21Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kawo karshen rikici a yankin gabas ta tsakiya ita ce samar da kasar Palasdinu da zata rayu kafada da kafada da haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Shugaban Palasdinawa Ya Yi Kira HKI Ta Dakatar Da Ginawa Yahudawa Gidaje A Yankunan Palasdinawa
Feb 16, 2017 11:47Shugaban Palasdinawa Mahmood Abbas ya bada sanarwar cewa yana goyon bayan sulhuntawa da HKi kan samar da kasashe biyu, inda a dayan bangaren kuma yake kiran gwamnatin yahudawan ta dakatar da gine gine a yankunan Palasdinawa da ta mamaye.
-
Isra'ila Ta Sake Dawo Da Batun Hana Kiran Sallah A Palastine
Feb 14, 2017 17:23Haramtacciyar kasar Isra'ila ta sake dawo da batun hana kiran sallah a cikin wasu yankunan Palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan kuma gabashin birnin Quds.