Pars Today
Hukumomi a Qatar sun bukaci masu shaguna dasu janye daga tsarin saye da sayar wa na kayan da ake shigowa dasu daga gungun kasashen da Saudiya ke jagoranta.
Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya ya yi furucin cin mutunci kan al'ummar Qatar ta hanyar bayyana cewar al'ummar Qatar ba su shige yawan mazauna hanya guda na kasar masar ba.
Ministan harkokin wajen Qatar, Sheikh Mohamed ben Abderrahmane Al-Thani, ya fada cewa kasarsa ba zata taba kasancewa karkashin mallakar Saudiyya ba.
Kasashen Habasha da Qatar sun tattauna kan hanyoyin karfafa matakan tsaro da na soji a tsakaninsu.
Ministan cikin gidan kasar Masar ya bayar da umarnin dage takunkumin bayar da visar gaggauwa ga 'yan kasar Qatar.
Shugaban majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah Sayyid Hashim Safiyyudin ya zargi Saudiyya da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Lebanon.
Kasashen Rasha da Qatar sun cimma yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ziyara da ministan tsaron Rasha Sergueï Choïgou, ya kai a birnin Doha.
Jaridar Kasar Qatar ta " al-Sharq" ta ambato ministan harkokin wajen kasar Najeriya -Geoffrey Onyeama yana kiran Saudiyya da ta kawo karshen takunkumin da ta kakabawa Qatar.
Ministan harkokin wajen kasar Italia ya bukaci kasashe larabawa 4 wadanda suka dorawa kasar Qatar takunkumai su kawo karshen hakan.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya bada labarin cewa: Mahukuntan Sudan da Qatar sun tattauna kan hanyoyin bunkasa alaka tare da taimakekkeniya a tsakaninsu.