Pars Today
Ministan al’adu na Isra’ila ya ce sun gina wani ramin karkashin kasa da ya hada Wadil Hulwa da kuma Babul Magariba da ke gefen masallacin Aqsa.
A taron shugabannin kungiyoyin musulmia birnin Istanbul na Turkiya an jaddada cewa masallacin Aqsa mai alfarma yana fuskantar gagarumar barazana daga yahudawan sahyuniya.
Wasu yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan masalalcin Quds mai alfarma, inda suka shiga cikin kofar magariba da ke yammacin harabar masalalcin.
Yahudawan Sahyuniya na ci gaba da aiwatar da sabon shirinsu na kawar da masallacin Quds baki daya cikin taswirar birnin.
Wasu yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun nemi yin kutse a yau a cikin harabar masallacin Quds mai alfarma, yayin da daruruwan masallata da ke cikin masallacin suka yi musu waigi.
Wani malamin yahudawa mai tsatsauran ra'ayi ya yi barazanar rusa masallacin Quds baki daya, matukar dai babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta birnin Quds ba ta amince da raba masallacin ba.