Wani Malamin Yahudawa Ya Yi Barazanar Rusa Masallacin Quds Mai Alfarma
(last modified Fri, 03 Jun 2016 09:06:02 GMT )
Jun 03, 2016 09:06 UTC
  • Wani Malamin Yahudawa Ya Yi Barazanar Rusa Masallacin Quds Mai Alfarma

Wani malamin yahudawa mai tsatsauran ra'ayi ya yi barazanar rusa masallacin Quds baki daya, matukar dai babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta birnin Quds ba ta amince da raba masallacin ba.

Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, Yahuda Glik wanda malamin yahudawa ne mai matsayin khakham, kuma dan majalisar Isra'ila ta Knesset, ya yi barazanar cewa, zai jagoranci yahudawa domin rusa masallacin Quds, matukar dai cibiyar palastinawa mai kula da harkokin addinin muslunci a birnin Quds ta ci gaba da biris da kiran da suka yi mata, na ta amince a raba masallacin Quds biyu, daya bangaren na musulmi, daya bangaren kuma na yahudawa.

 

Wannan furuci dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga bangarori daban-daban na musulmi, kamar yadda a nasa bangaren babban malami mai bayar da fatawa a birnin Quds Sheikh Ikrama Sabri ya yi Allawadai da wannan furuci da ya fito daga bakin daya daga cikin malaman yahudawa kuma dan siyasa, inda ya ce wannan furuci ne mai matukar hadari, wanda al'ummar palastinu da sauran musulmin duniya ba za su taba amincewa da shi ba.

 

Sheikh Ikrama ya kara da cewa, duk abin da yake faruwa da sanin gwamnatin Isra'ila ne, domin kuwa ita ce take bayar da kariya ga yahudawa masu tsatsauran ra'ayi da suke cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na addinin musulunci, da hakan ya hada har da masallacin Quds mai alfarma, kuma alkiblar musulmi ta farko.