-
Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Aka Mata
Sep 15, 2016 05:53Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta yi watsi da wani rahoton da wani mai kare hakkokin bil'adaman dan’adam nan George Clooney, ya fitar inda ya zargi gwamnati da ‘yan tawayen kasar da cin hanci da rashawa da kuma amfani da yaki da rikicin da ke faruwa a kasar don azurta kansu.
-
EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Da Kuma Wani Na Kurkusa Da Jonathan
May 17, 2016 17:59Rahotanni daga Nijeriya suna bayyana cewar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annuti (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero da kuma tsohon sakataren kashin kai na tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, Hasan Tukur bisa zargin sama da fadi na wasu makudan kudade.
-
EFCC Ta Tsare Mal. Shekarau Saboda Zargin Cin Kudaden Makamai
May 13, 2016 18:10Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilmi na kasar Malam Ibrahim Shekarau saboda zarginsa da hannu cikin cin wasu kudade da suka kai Naira miliyan 950 da aka ware don sayo makaman fada da kungiyar Boko Haram a kasar.
-
Nijeriya Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Firayi Ministan Birtaniyya Kan Cin Hanci A Kasar
May 11, 2016 05:29Fadar shugaban kasar Nijeriya ta yi watsi da kalaman firayi ministan Birtaniyya David Cameroon na bayyanar kasar a matsayin kasar da cin hanci da rashawa yayi mata katutu tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abin baki ciki.
-
'Yan Majalisar Brazil Sun Amince A Ci Gaba Da Shirin Tsige Shugaba Rousseff
Apr 18, 2016 04:26Rahotanni daga kasar Brazil sun bayyana cewar 'yan majalisar dokokin kasar sun amince da ci gaba da shirin tsige shugabar kasar Uwargida Dilma Rousseff a daidai lokacin da magoya baya da kuma masu adawa da shugabar suke ci gaba da zanga-zangogi a kan titunan kasar.
-
Firayi Ministan Iceland Ya Yi Murabus Saboda Tonon Sililin Panama
Apr 06, 2016 05:37Rahotanni daga kasar Iceland sun ce firayi ministan kasar Sigmundur David Gunnlaugsson ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon bankado abun kunya na kauce biyan kudaden haraji da haramta kudin haramun da wani kamfani na kasar Panama yayi.