Firayi Ministan Iceland Ya Yi Murabus Saboda Tonon Sililin Panama
Rahotanni daga kasar Iceland sun ce firayi ministan kasar Sigmundur David Gunnlaugsson ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon bankado abun kunya na kauce biyan kudaden haraji da haramta kudin haramun da wani kamfani na kasar Panama yayi.
Rahotannin sun ce firayi ministan ya ajiye aikin nasa ne kwana guda bayan wani gangami na dubban al'ummar kasar na neman ya sauka daga mukamin nasa bayan bankado sirrinsa da aka yi na cewa yana daga cikin jami'ai da manyan masu kudi na duniya da suke amfani da kamfanoni na kasashen ketere domin kauce biyan kudaden haraji da kuma halalta kudaden haramun.
Wannan mataki da firayi ministan na Iceland ya dauka ya sanya shi zama mutum na farko daga cikin jami'an gwamnati da manyan 'yan kasuwa da wannan tonon sililin ya ritsa da shi.
A shekaran jiya ne dai wasu kafafen watsa labarai su bayyana samuwar wasu takardun bayanan asiri da aka fitar daga kasar Panama da ke nuna cewar manyan ‘yan siyasar duniya, da wasu fitattun mutane na boye tarin dukiyarsu a wasu kasashe don kaucewa biyan haraji da kuma halatta kudaden haramun.
Daga cikin mutanen da sunayensu suka fito cikin takardun, wadanda ko dai suke da hannu kai tsaye ko kuma wasu na kurkusa da su sun hada har da shugaban kasar Rasha, firayi ministan Birtaniyya, tsohon sarkin Saudiyya Abdullah, bugu da kari kan wasu shugabannin Afirka da manyan jami'an gwamnati ciki kuwa har da shugaban majalisar dattawan Nijeriya na yanzu Bukola Saraki da na da David Mark.