Pars Today
Dazu da rana ne dai jiragen yakin Saudiyya su ka kai hari a kan ginin ofishin shugaban kasar Yemen da ke birnin San'aa.
Jiragen yakin Libiya sun yi ruwan bama-bamai kan maboyar 'yan ta'adda a garin Derna na kasar Libiya
Sojojin Yamen sun bude wuta kan gungun sojojin marautar Saudiyya a yankunan Jizan da Asir da suke kudancin kasar ta Saudiyya, inda suka kashe sojoji akalla bakwai.
A daren jiya Talata, Jiragen yakin kawancen Saudiya sun yi ruwan bama-bamai har sau biyar a yankunan Shu'ub da bani Hashish na gabashin Sana'a babban birnin kasar Yemen.
Asusun kananan yara na MDD ta bakinsa shugabansa na arewacin Afirka ya ce;Kawo ya zuwa yanzu kananan yara 5000 Saudiyya ta kashe a cikin kasar Yemen
A daren jiya litinin, jiragen yakin kawancen saudiya sun yi luguden wuta kan fadar shugaban kasar Yemen a birnin San'a.
A daren jiya juma'a ne dai jiragen yakin suka kai harin a kan ma'aikatar tsaron Yamen dake birnin San'aa har sau biyu.
A jiya talata ne sojojin Yemen da kuma dakarun sa-kai na Ansarullah suka kai harin da manyan bindigogi a sansanonin Saudiyya na al-majazah da Riqabatul Hanjar da ke gundumar Asir.
Wani jami'in gwamnatin HKI ya ce idan jumhoriyar musulinci ta Iran ta ci gaba da karfafa matsayinta a siriya, to isra'ila za ta yi lugudar wuta a kan fadar shugaban kasar Siriya.
Gwamnatin kasar Algeria ta yi kira ga kasar masar da ta dakatar da kai hare hare a gabancin kasar Libya, don hakan ba zai warware matsalolin tsaron da kasar take fama da su ba.