HKI Ta Yi Barazanar Kai Hari Kan Fadar Shugaban Kasar Siriya
Wani jami'in gwamnatin HKI ya ce idan jumhoriyar musulinci ta Iran ta ci gaba da karfafa matsayinta a siriya, to isra'ila za ta yi lugudar wuta a kan fadar shugaban kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto jaridar Jerusalem Post ta Sahayuna ta ambato wani jami'in HKI da ya bukaci da sakaye sunansa na yiwa kasar Rasha barazanar cewa matukar ba a samu canji a yankin ba, to birnin tel aviv zai yi dukkanin kokarinsa na ruguza yarjejjeniyar tsagaita wuta da kasashen Rasha da Amurka suka cimma a kudancin kasar siriya.
Jami'in ya amince da cewa babu wata matsaya da aka cimma tsakanin Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin da Piraministan HKI Benjamin Netanyahu a tattaunawar da suka yi ranar Larabar da ta gabata.
Bisa rahoton bayan ganawar, an bayyana cewa Netanyahu ya fadawa Putin cewa matukar dai bai yi la'akari da damuwar Tel-Aviv ba to Isra'ila za ta shiga yaki da Siriya.
Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da mahukuntan HKI ke nuna damuwa game da yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a kudancin kasar Siriya, inda suka tabbatar da cewa wannan yarjejjeniya za ta sanya kasar Iran ta kara samun gindin zama da karfi a Siriya.