Netanyahu Ya Yi Barazanar Daukan Matakin Soja Kan Yankin Zirin Gaza
Piraministan Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya yi barazanar kai hare-hare a yanklin zirin Gaza na Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Meher a wannan juma'a ya nakalto Piraministan haramtacciyar kasar Benjamin Netanyahu yayin da yake wani ran gani a yankunan kan iyakar Isra'ila da yankin Zirin Gaza na cewa matukar dai yarjejjeniyar zaman lafiya ba ta tabbata a yankin zirin Gaza ba, zai dauki matakin fadada kai hare-hare a yankin.
Dangane da wannan batu, jaridar Al-arabe ta kasar Qatar ta habarta cewa Piraministan Isra'ilan ba shi da wani zabi face ya amince da jadadda yarjejjeniyar zaman lafiya da yankin zirin Gaza, ganin cewa zaben 'yan majalisa na kara kuratowa, kuma a iri wannan yanayi ba zai yarda ya bude wani yaki da kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa ba.
A cikin 'yan kwanakin nan ake sa san za a gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasar Masar da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas domin sake duba yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa da Isra'ila.
A watan Dicembar 2017 ne mahukuntan Isra'ila suka fara kai wani sabon hare-haren ta'addanci kan al'ummar yankin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahada da kuma jikkata dubun dubutan Palastinawa.
A matsayin mayar da martani kungiyar gwagwarmaya ta Palastinu ta harba makamai masu linzami da rokoki sama da 500 zuwa cikin Haramtacciyar kasar Isra'ila, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da kuma jikkatar yahuwa 'yan kama wuri zauna da dama.