Feb 26, 2019 17:49 UTC
  • An Yankewa Wani Tsohon Minista A HKI Zaman Kaso Saboda Aikin Leken Asiri Wa Kasar Iran

Wata kotun HKI ta daure tsohon ministan makamashi na haramtacciyar kasar Gonen Segev shekaru 11 a gidan kaso bayan ya amince da cewa ya yi aikin leken asiri wa kasar Iran.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta bayyana cewa kotun ta yankewa tsohon ministan hukuncin ne bayan ya amince da laifinsa, sannan mai gabatar da kara laifuffukansa ya janye sauran tuhume-tuhime da ake masa. 

Mai gabatar da kara a kotun da ke birnin Qudus, Geula Cohena ya bayyana cewa Segev yayiwa kasar Iran aikin leken asiri har na shekaru biyar. Sannan ya je kasar Iran har sau biyu. Banda haka tsohon ministan ya sha haduwa da jami'an gwamnati da hukumomin leken asirin kasar Iran a kasashen da dama a duniya.

Labarin ya kara da cewa tsohon minisyan ya sha karban kayakin sadarwa na leken asiri a hannun Iraniywan sannan har ya taba buya wayar tarho zuwa ofishin jakadancin kasar Iran da ke Abuja na tarayyar Najeriya.

Tags