-
Iran Ta Yi Ruwan Makamai Masu Linzami Na Maida Martani Kan Harin Ahwaz
Oct 01, 2018 05:39Dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Jamhuriya Musulinci ta Iran, sun sanar da kai hare hare na makamai masu linzami kan wani babban sansanin 'yan ta'adda a gabashin Siriya, a matsayin maida martani kan harin da aka kai a birnin Ahwaz.
-
Fara Mika Makamin Kariyar Nan Na S-300 Ga Gwamnatin Kasar Siriya
Sep 30, 2018 05:52Batun harbo jirgin saman yakin kasar Rasha a kasar Siriya da aka yi, wanda Rashan ta dora alhakin hakan gaba dayansa kan haramtacciyr kasar Isra'ila ya dau wani sabon salo da kuma isar da wani sako wanda ba a yi tsammaninsa alal akalla a wannan lokacin ba. Mahunta a kasar Rashan dai sun bayyana cewar an harbo jirgin ne sakamakon yadda sojojin 'Isra'ilan' suka fake da wannan jirgin wajen kai hari kan wasu cibiyoyi na kasar Siriya.
-
Kasar Aljeriya Ta Jaddada Cewa Tana Ci Gaba Da Goyon Bayan Gwamnatin Siriya
Sep 29, 2018 11:56Ministan harkokin wajen kasar Aljariya ya jaddada cewa: Gwamnatin kasarsa tana ci gaba da goyon bayan gwamnatin Siriya a kokarin da take yi na ganin ta warware rikicin kasarta da kanta.
-
Rasha Ta Sanar Da Fara Mika Makamin Kariyar Nan Ta S-300 Ga Kasar Siriya
Sep 29, 2018 05:55Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar kasarsa ta fara mika makamin kariyar nan ta S-300 ga kasar Siriya a ci gaba da kokarin da suke yi na tabbatar da tsaron kasar da kuma ba da kariya ga sojojin Rashan da suke kasar Siriya.
-
Michel Aoun: Shigar Hizbullah A Syria Bai Saba Wa Ka'ida Ba
Sep 26, 2018 07:01Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun ya bayyana cewa, shigar mayakan kungiyar Hizbullah a cikin kasar Syria bai saba wa ka'ida ba.
-
Isra'ila Ta Damu Da Shirin Rasha Na Mikawa Siriya Makaman S-300
Sep 25, 2018 17:49Mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila sun nuna matukar damuwarsu akan shirin kasar Rasha na mallakawa gwamnatin Bashar Al'Assad na Siriya makaman garkuwa na hare haren sama kirar S-300.
-
Rasha Za Ta Mikawa Siriya Makaman Garkuwa Na S-300
Sep 24, 2018 11:05Kasar Rasha ta sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta mikawa gwamnatin Siriya makaman garkuwa na S-300.
-
Rasha: Isra'ila Ce Take Da Alhakin Harbe Jirgin Yakin Kasar Rasha
Sep 23, 2018 17:42Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta gabatar da cikakken rahoto dangane da yadda aka harbo jirgin yakin kasar a lardin Lazikiyya na kasar Siriya tana mai dora alhakin faruwar hakan a wuyanharamtacciyar kasar Isra'ila.
-
Putin: Harin Da Isra'ila Ta Kai Siriya, Keta Hurumin Kasar Ne
Sep 19, 2018 05:33Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar hare-haren da haramtacciyar kasar Isra'ila take kai wa kasar Siriya keta hurumin kasar Siriya yana mai, yana mai jan kunnen Isra'ilan da ta guji duk wani abin da zai sanya rayuwar sojojin Rashan da suke Siriya cikin hatsari.
-
Gwamnatin Sahayoniya Ta Yi Barazanar Kashe Shugaban Kasar Siriya
Sep 17, 2018 19:07Ma'aikatar Yakin Sahayoniya ta watsa wasu hotuna tare da da'awar cewa wurin rayuwar Bashar Al-Asad ne inda ta yi barazanar hallaka Shugaban kasar ta Siriya