-
Sojoji Masu Bore A Ivory Coast Sun Kai Hari Da Kona Wani Barikin Soji
Jan 11, 2018 05:48Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar wasu sojoji masu bore a garin Bouake, gari na biyu mafi girma a kasar, sun kai hari kan wani barikin zaratan sojojin kasar da ake kira da CCDO a garin a daren jiya inda suka kwashi makamai da kuma sanya wuta a wasu bangarori na barikin
-
Rundunar Sojin Ivory Coast Ta Sha Alwashin Aiki Da Gwamnatin Kasar A Wannan Sabuwar Shekara Ta 2018
Jan 05, 2018 11:54Babban hafsan hafsoshin rundunar sojin Ivory Coast Janar Seko Ture ya bayyana cewa rundunar sojin kasar a shirye take ta bada hadin kai ga gwamnatin kasar.
-
Syria: Sojojin Sun Bude Kai Hare-hare Akan Rundunar "Jaishul-Islam"
Jan 01, 2018 18:55Sojojin Syria sun fara kai harin ne a yankunan Huzrama da Zuraify da suke gabacin da birnin Damashka, da mayakan "JaishulIslam' suke da sansani
-
Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Sanar Da Nasarar Dakile Kokarin Juyin Mulki A Kasar
Dec 31, 2017 05:53Mahukunta a kasar Equatorial Guinea mai arzikin man fetur sun sanar da samun nasarar dakile wani kokari na juyin mulki da kifar da gwamnatin shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasago, wanda shi ne shugaban da ya fi kowa dadewa bisa karagar mulki a Afirka.
-
Shugaba Buhari Ya Tsawaita Wa'adin Shugabancin Manyan Hafsoshin Sojojin Nijeriya
Dec 19, 2017 05:36Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya amincewa da tsawaita wa'adin shugabancin manyan hafsan hafsoshin sojin kasar saboda kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram.
-
Syria: Amurka Tana Kafa Sabuwar Rundunar Mayaka
Dec 16, 2017 19:11Cibiyar kasar Rasha mai kula sulhu na kasar Syria ta sanar da cewa Amurkan tana kafa sabuwar rundunar soja a sansanin 'yan gudun hijira na Hasaka da ke arewa maso gabacin kasar.
-
Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Boko Haram daga Garin Magumeri Bayan Sun Kwace Shi
Nov 26, 2017 17:20Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewar dakarunta sun fatattaki 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram daga garin Magumeri da ke kimanin kilomita 50 daga birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno bayan da 'yan kungiyar suka kwashe garin a jiya Asabar.
-
Syria: Sojoji Sun Sake 'Yanto Wasu Garuruwa Biyu A Arewacin Gundumar Hamah
Nov 13, 2017 18:54Sojojin na kasar ta Syria sun sanar da kwace kauyukan biyu ne daga hannun kungiyar 'yan ta'adda ta al-Nusrah a yammancin kasar.
-
An gano ramuka dauke da gawarwaki 400 a Iraki
Nov 12, 2017 05:51Gwamnan jihar Karkuk na kasar Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija, inda a nan ne aka fatattaki mayakan kungiyar IS a makon da ya gabata.
-
Sojojin Syria Sun Rusa Wuraren Harba Makamai Masu Linzami Na 'Yan Ta'adda A Halab.
Oct 12, 2017 06:24Tashar telbijin din al'alam ta bada labarin cewa a jiya laraba ne sojojin na Syria sun kai harin ne a yankunan Lirmon da Rashidin da ke kusa da Halab.