Syria: Amurka Tana Kafa Sabuwar Rundunar Mayaka
(last modified Sat, 16 Dec 2017 19:11:41 GMT )
Dec 16, 2017 19:11 UTC
  • Syria: Amurka Tana Kafa Sabuwar Rundunar Mayaka

Cibiyar kasar Rasha mai kula sulhu na kasar Syria ta sanar da cewa Amurkan tana kafa sabuwar rundunar soja a sansanin 'yan gudun hijira na Hasaka da ke arewa maso gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya kuma ambato shaidun ganin ido a tsakanin 'yan hijira da suka koma gidajensu a yankin suna cewa; Bayan bada horon da sojojin Amurka suka yi musu, suna umartarsu da su yaki sojojin gwmanatin Syria.

Tun watanni shida da suka gabata ne dai sojojin na Amurka suka fara bada horo ga wasu mutane a yankin Hasakah, da kawo ya zuwa yanzu sun kai 750, sun kuma kunshi 'yan ta'addar Dae'sh 400 da Amurkan ta taimakawa suka fice daga garin Rikkah a watan Oktoba.

Amurka ta kafa kawancen da ta kira na kasa da kasa da sunan fada da ta'addanci, sai dai kawancen na Amurka ya zama mai taimakawa 'yan ta'adda.